Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Bani Isra'ila Sun Fara Rarraba Takardun Umurnin Ficewa Daga Zirin Gaza Ga Dubban Yahudawa 'Yan Kaka-Gida


Isra’ila ta aika da dubban sojojinta zuwa zirin Gaza domin rarraba takardun umurnin barin yankin nan da jibi laraba ga 'yan Isra'ila su dubu takwas da dari biyar.

Sojoji da ’yan sanda sun yi niyyar shiga dukkan unguwannin kwace-ka-zauna na yahudawa guda 21 dake zirin na Gaza domin raba wadannan takardun. Amma kuma wasu matasa masu yin adawa da shirin janye yahudawan, sun toshe hanyoyin shiga unguwanni biyar, suka hana kowa shiga.

Mazauna unguwar share-ka-zauna ta yahudawa mai suna Neve Dekalim, wadanda suka nuna fusata, sun yi ta kona tayoyi suka kuma yi kawanya da juna domin hana shiga cikin wannan unguwa.

Jami’an sojin Isra’ila sun yi gargadi cewa daga ranar laraba zasu yi amfani da karfin soji su fitar da wadanda suka rage a yankin.

Firai minista Ariel Sharon ya tsaida shawarar janyewa daga yankin bara da cewa yana da tsadar gaske a samar da kariya ga mutane dubu takwas da dari biyar dake zaune a yankin, wadanda Palasdinawan Gaza su fiye da miliyan daya suka kewaye. A shekarar alib dari tara da sittin da bakwai ne Isra’ila ta kwace zirin Gaza lokacin yakin gabas ta tsakiya.

XS
SM
MD
LG