Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Jumma'a Majalisar Dokokin Burundi Zata Zabi Sabon Shugaban Kasa


Sabuwar majalisar dokokin Burundi, tana shirin zaben shugaban kasar a gobe jumma’a, a yayin da wannan ’yar karamar kasa take kokarin cimma zaman lafiya bayan yakin basasar shekaru 12.

Ana sa ran cewa tsohon madugun ’yan tawayen Hutu, Pierre Nkurunziza, zai samu kashi biyu bisa uku na kuri’un ’yan majalisa da ake bukata domin zamowa shugaban kasa. Shi kadai ne dan takarar dake neman wannan kujera.

Idan har aka zabe shi, Mr. Nkurunziza zai zamo shugaban Burundi na farko tun 1993 lokacin da yakin basasa ya barke a bayan da aka kashe shugaban kasar na farko dan kabilar Hutu da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

Mr. Nkurunziza ya ce manufarsa ta hada kan kabilun kasar, da shigar da kowa da kowa cikin harkar siyasa da kuma yaki da talauci sune suka janyo masa farin jini da goyon baya.

An kashe mutane fiye da dubu 250, akasarinsu fararen hula, a lokacin yakin kabilancin da aka yi a tsakanin kabilun Hutu da Tutsi na kasar Burundi.

XS
SM
MD
LG