Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Madugun 'Yan Tawayen Kabilar Hutu Ya Zamo Shugaban Kasar Burundi


An zabi wani tsohon madugun ’yan tawayen kabilar Hutu, Pierre Nkurunziza, a zaman sabon shugaban kasar Burundi, a matakin karshe na aiwatar da shirin zaman lafiyar da aka tsara da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru 12.

A yau jumma’a aka zabi Mr. Nkurunziza da gagarumin rinjaye a majalisar dokoki. A zahiri ma duk ’yan takarar dake kwadayin wannan kujera sun janye a bayan da jam’iyyar Mr. Nkurunziza ta FDD ta samu gagarumin rinjaye a zaben ’yan majalisar dokoki da aka yi kwanakin baya.

A bayan da aka zabe shi, Mr. Nkurunziza ya roki dukkan ’yan kasar Burundi da su taimaka wajen sake gina kasar. A ranar 26 ga watan nan na Agusta ne za a rantsar da shi a zaman shugaban kasar.

Sabon shugaban mai shekaru 40 da haihuwa, zai zamo shugaban kasar Burundi na farko da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya tun bayan barkewar yakin basasa a 1993. An gwabza wannan yakia tsakanin ’yan kabilar Hutu masu rinjaye a kasar da kuma ’yan kabilar tsiraru ta Tutsi wadanda suka kanainaye harkokin siyasar Burundi. An ce mutane kimanin dubu 300, akasarinsu fararen hula, suka mutu a wannan yaki.

XS
SM
MD
LG