Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Mulkin Kan Falasdinawa Ta Kafa Dokar Da Ta Ba Ta Mallakin Dukkan Filaye Da Kuma Kadarorin Da 'Yan Kaka-Gida Zasu Bari A Zirin Gaza


Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanya hannu kan wata doka, wadda ta bai wa gwamnatinsa ikon mallakin dukkan filaye da kadarorin da yahudawa ’yan kama-wuri-zauna zasu bari a zirin Gaza da kuma wani bangaren yankin yammacin kogin Jordan.

Akwai gidaje da unguwannin Falasdinawa a wadannan yankuna kafin Isra’ila ta kwace su, kuma Malam Abbas ya nada wani kwamitin ministoci domin nazarin dukkan takardu da ikirarin mallakar filayen da Falasdinawan da aka kora daga yankin zasu gabatar.

Ya zuwa tsakar ranar jumma’a, sojojin Isra’ila sun kwashe mazauna unguwannin share ka zauna na yahudawa guda 17 daga cikin 21 dake zirin Gaza. A yankin yammacin kogin Jordan, ’yan kaka gida sun fice domin radin kansu daga unguwanni biyu daga cikin guda hudun da aka yi niyyar mayarwa da Falasdinawa kayansu. A cikin mako mai zuwa za a kwashe mazauna sauran unguwanni biyun.

Majalisar mulkin kai ta Falasdinmawa ta ce da zarar an rushe gidajen yahudawa da aka gina a yankin, to zata gina benaye masu yawa domin taimakawa wajen samar da matsuguni ga mutane fiye da miliyan daya dake zirin na Gaza.

XS
SM
MD
LG