Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Sojojin Bani Isra'ila Sun shiga Unguwannin Share-Ka-Zauna Hudu Domin fitar Da Yahudawan Dake Cikinsu


Dubban sojojin bani Isra’ila wadanda ba su dauke da makami, sun shiga cikin wasu unguwannin share-ka-zauna na yahudawa guda hudu yau lahadi, a wani yunkuri na kammala kwashe ’yan Isra’ila dake yankin na Falasdinawa cikin wannan makon.

Motocin buldoza na sojoji sun karya kofar shiga unguwar share-ka-zauna ta Katif, inda yahudawa ’yan kama wuri zauna da magoya bayansu suka cinna wuta a shara da tayoyin motar da suka yi shingaye da su domin hana kowa shiga.

Jim kadan a bayan wannan ne sai sojojin suka shiga wata unguwar ta manoma mai suna Atzmona, wadda ke dauke da daruruwan ’yan kama wuri zauna. ’Yar tazara kadan daga kofar shiga unguwar, wasu matasa da suka yi gungu sun yi ta rera taken cewar yahudawa ba su korar yahudawa.

An bayar da rahoton tankiya sosai amma kuma babu wani tashin hankalin da aka samu.

A zauren taron majalisar zartaswarsa na mako-mako a yau lahadi, firayim minista Ariel Sharon yayi tur da yahudawa ’yan tsagera dake kai hare-hare a kan sojoji da ’yan sanda, yana mai bayyana su a zaman ’yan daba. Har ila yau firayim ministan ya ja kunnen ministocin dake neman bijirewa, yana mai fadin cewa duk mai niyyar yin murabus yana iya yi. Daga nan ne sai majalisar zartaswar ta amince da kwashe mutanen dake cikin sauran unguwannin da aka yi niyyar rushewa a zirin Gaza da yankin Yammacin kogin Jordan.

A gobe litinin za a fara kwashe mutanen dake cikin unguwar Netzarim, unguwa mafi girma ta yahudawa a Zirin Gaza.

A shekarar da ta shige Mr. Sharon ya fara gabatar da shawarar janyewa daga Gaza, yana mai fadin cewa Isra’ila tana kashe kudi mai dan karen yawa wajen kare unguwanni guda 21 dake Gaza, inda yahudawa kasa da dubu 9 ke zaune a tsakiyar Falasdinawa fiye da miliyan daya. Isra’ila ta kwace zirin na Gaza kusan shekaru 40 da suka shige.

XS
SM
MD
LG