Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Hukumar Bincike Ta Tarayya Na Amurka Sun Binciki Gidan Atiku Abubakar A Washington


Jami'an bincike na tarayya a nan Amurka sun binciki gidan mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ke wajen birnin Washington, a wani bangare na binciken cin hanci da rashawa da ake yi.

Wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada yau lahadi cewar an binciki gidan an Atiku Abubakar a ranar 3 ga watan Agusta. Sai dai ta ki yarda ta bayar da karin bayani. Ita ma ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ki yarda ta ce uffan a game da wannan batu.

Jami'an bincike na tarayya sun binciki gidan Atiku Abubakar a ranar da suka binciki gidajen wani dan majalisar tarayya ta nan Amurka, William Jefferson, a nan Washington da kuma New Orleans a Jihar Louisiana. Shi dai wannan dan majalisa dan jam’iyyar democrat ne wanda sau takwas ana zabensa kan wannan kujera daga jihar ta Louisiana.

Wata jarida ta birnin New Orleans ta bayar da rahoto jiya asabar cewa jami’an da suka binciki gidan dan majalisa Jefferson suna neman takardu ne dangane da wata harkar kamfanin sadarwa ta wayar tarho da yake kokarin kafawa a Nijeriya.

Jaridar ta ce jami’an suna neman shaidar toshiyar bakin da aka yi zargin cewar Mr. Jefferson ya bayar da kansa, ko kuma ya sa aka bada Atiku Abubakar, da kuma mataimakin shugaban kasar Ghana, Alhaji Aliyu Mahama. An binciki gidan dan majalisar wakilan kimanin makonni uku a bayan da ya komo daga tafiya zuwa kasar Ghana.

XS
SM
MD
LG