Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu Ta Yi Watsi Da Kokarin Shiga Tsakani A Rikicin Ivory Coast


Afirka ta Kudu ta ce zata watsar da kokarin shiga tsakani a kasar Ivory Coast dake rarrabe a bayan da aka sake samun jinkirin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tare da kiran da a jinkirta zabe. Sassan masu fada da junansu a yanzu su nna fargabar cewa ba za a iya warware wannan rikici ta hanyar lumana ba.

Wakilin Muryar Amurka ya ce a can birnin Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu, mukaddashin ministan harkokin waje, Aziz Pahad, ya ce kasarsa tana kammala kokarinta na shiga tsakani, kuma zata mika alhakin wadannan ayyuka a hannun Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce 'yan tawayen arewacin Ivory Coast da kuma 'yan adawar siyasa sun ki yarda su aiwatar da alhakin da ya rataya wuyansu karkashin yarjejeniyar, duk da cewa shugaba Laurent Gbagbo ya yarda da abinda ya kira shwarwarin Afirka ta Kudu.

Mr. Pahad ya bayyana cikas din da ake samu a zaman "dogon turanci kawai." Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna wannan batu larabar nan a New York, inda sassan na kasar Ivory Coast suke fuskantar barazanar takunkumi a saboda sun kasa aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka fara kullawa a farkon shekarar 2003 a Faransa.

'Yan tawaye da 'yan adawar siyasa sun ce shugaba Gbagbo ya kasa yin aiki da yarjejeniyar, ta hanyar sauya wasu bangarorin yarjejeniyar har ta zamo maras ma'ana, haka kuma ya kasa kyalewa a gudanar da zaben da aka shirya yi ranar 30 ga watan Oktoba ba tare da ha'inci ba.

Sun yi kiran da a cire Mr. Gbagbo daga kan karagar mulki a kafa gwamnatin rikon kwarya.

XS
SM
MD
LG