Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye Da Dari Shida Sun Mutu A Iraqi


Daruruwan 'yan Shi'a sun mutu a sanadin rudanin da ya biyo bayan rade-radin cewar wani dan kunar-bakin-wake ya shiga cikin daruruwan dubban mahajjatan dake ziyarar masallacin Imam Musa al-Khadimi dake Bagadaza.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraqi ta ce akasarin wadanda suka mutu a wannan ture-ture na yau laraba mata ne da yara kanana, kuma akasari sun mutu a bayan da aka tattake su ko kuma suka fada ruwa nya cinye su a kogin Tigris.

Ma'aikatar ta ce ya zuwa tsakar rana, mutane 647 (dari shida da arba'in da bakwai) suka mutu, wasu fiye da 300 (dari uku) kuma suka ji rauni.

Wani shingen dake kan gadar da mahajjatan su kimanin miliyan daya ke wucewa ta kai, ya tsinke, daruruwan mutane suka fada kasa cikin kogin Tigris.

Wannan al'amari ya faru a lokacin da wadannan mahajjata suke kan hanyar zuwa masallacin domin karrama mutuwar daya daga cikin njigogin 'yan mazhabin Shi'a, Imam Musa al-Khadimi, wanda ya mutu a cikin karni na 8.

'Yan sandan Iraqi sun ce watakila wani a cikin taron ne ya fara kururuwar cewar dan harin bam na kunar-bakin-wake ya shigo cikin jerin mutane, sai kowa ya firgita, aka fara ture-ture, har aka tattake wasu, kuma wannan shinge dake kan gada ya btsinke mutane suka yi ta fadawa cikin kogi.

An yi ta kwasar wadanda suka ji rauni zuwa asibitocin dake birnin. Wani asibiti ma ya ce akwai ngawarwakin mutane fiye da 100, yayin da wasu da kakakin bai san adadinsu ba sun bayyana da raunuka.

Gwamnatin Iraqi ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku.

XS
SM
MD
LG