Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Husni Mubarak yaci zabe


Shugaba Husni Mubarak, mutumin dayake shugabancin kasar Misra tun wajen shekara ta 1981, bayan kisar shugaba Anwar Sadat, shine ya lashe zaben da aka yi.

Shi dai Mr. Mubarak wanda ’yan kasar ke masa taken zaki ko kuma Fir’unan karshen zamani, yayi shugabancin da ba’a taba sauya salonsa ba a kasar har na tsawon shekaru 24. Bayan wannan sabon zaben zai sake rike karagar mulkin kasar har na tsowon shekaru 6 nan gaba. A watan Fabarairu ne ya umurci ’yan majalisar dokokin kasar akan su gyara tsarin mulkin kasar domin ya baiwa jam’iyun siyasa da dama ikon tsayawa zabe.

‘Yan adawa a kasar sun soki jam’iyarsa ta "National Democratic" da laifi janyo rashin aikin yi a kasar da kuma rashin gyare-gyare ta fuskar siyasa. Wannan shugaba shekarunsa 77 ne da haifuwa. Masu goyon bayan jam’iyar tasa sunce ya jagoranci kasar na tsawon shekaru fiye da 20, ba tare da wata kasa ta tsokani kasarsu da yaki ba.

Kafin ya hau karagar mulkin kasar Masar, Shugaba Mubarak, hafsan mayakan saman kasarne a wajen shekata ta 1972, daga baya aka nadashi mataimakin shugaban kasar Masar, kafin ya gaji kujerar daga marigayi Anwar Sadat.

XS
SM
MD
LG