Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Majalisar dinki duniya bayan shekaru 60


Shugabannin kasashen Duniya wajen 150 sun hallara a birnin NY domin fara taron kolin MDD na kwanaki uku da za’ayi domin bukin cika shekaru 60 da kafuwar majalisar. Wannan taro wanda tunin aka farashi yau Laraba yana dauke da jawabai da Babban sakataren Mjalisar Dinkin Duniya Koffi Annan da kuma shugaban Amirka George Bush za su yi. Shugaba Bush zai kuma kebanci domin ganawa da firayiministan Isra’ila Ariel Sharon da kuma Firayiministan Biritaniya Tony Blair akan batutuwn dangantaka tsakanin Amirka da kasashensu. Ana sa rai shugabanni a wannan taro na kwanaki uku zasu amince da wani daftarin kuduri mai shafi 35 na gyara da zai maida hankali ga shirye-shiryen kawar da talauci a duniya, da kuma matakan garambawul a Majalisar. To amma wannan daftari da taron wakilan Majalisar suka sanya masa hannu jiya Talata, bayanda suka shafe makonni suna muhawara akai, ana ganinsa amatsayin wanda zai fi saukin samun aminci akan wanda ada kakakin Majalisar Koffi Annan ya tsara ya gabatar. An share wani sashi na daftarin dake kira akan a kwance damarar yaki da kuma hana yaduwar makamai, da kuma wani harafi dake baiyana ayyukan ta’addanci, daga cikin wannan daftarin da za’a gabatar. Tunin dai MR. Annan ya soki wasu kasashe da ya kira ‘yan lelen wasu kasashe da laifin kin bada kai bori ya hau.

XS
SM
MD
LG