Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Kirada da'a Yiwa Majalisar Dinkin Duniya Garambawul


Shugabannin kasashen duniyan da suka yi jawabbai yau a rana ta biyu da fara babban taron MDD sunyi kira da ayiwa majalisar garambawul tayadda zata iya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta’addanci. Shugaba Hu Jintao na China da shugaba Vladimir na Rasha duk sun ce kamata yayi MDD ta zama itace a sahun gaba wajen wannan gwagwarmayar. Shi kuma a nasa jawabin, shugaban Iraq Jalal Talabani cewa yayi demokradiya da ‘yanci wajibai ne wajen karfafa tattalin arzikin kasashe, yayinda frayim ministan India Manmohan Singh yace MDD na bukatar garambawul ba karami ba, don har yanzu aiki take kamar ana a cikin shekara ta 1945 (lokacinda aka kafa ta). Frayim-ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan kuma yace al’ummar duniya ce baki daya zata anfana daga duk wata kwaskwarimar da za’ayi wa MDD.

Su kam shugabannin kasashen Afrika, abubuwan da aka saba ji daga bakunansu, a bana ma sune aka ji suna maimaitawa – kamar yaki da talauci, rikon a yafe musu bashi da batun yiwa MDD wasu ‘yan chanje-chanje. Jagabannin kasashen na Afrika da suka fara jawabbai sun hada da shugaban Djibouti, Ismail Omar Guelleh da na Zambia, Levy Mwanawasa, wadanda su duka biyu suka ce har yanzu suna da tazara mai nisa kafin su cimma burin da suka shata shekaru 5da suka wuce nashawo kan masifar talauci dake addabar al’ummarsu da kuma bunkasa sha’nin ilmi. Shugaban kasar Gambia ne wkawai, Yayah Jammeh yace kasarsa ta sami wani ci gaba a wannan yakin da suke da talauci. Shi kuma shugaba Thabo Mbeki na ATK fada yake cewa banbancin dake tsakanin attajiran kasashe da na matalauta ne ne ke sa su matalautan basa iya cimma muradunsu. Jin haka shi kuma PM Denmark, Anders Fogh Rasmussen yayi kira akan su attajiran kasashen da su dada tallafawa matalautan kasashen Afrika, musamman ma wajen yaki da cuttuttukka kamar AIDS. Sai dai suma kasashen Afrikan yace dole su mike su yaki cin hanci da rashawan da yayi musu katutu.

XS
SM
MD
LG