Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yace Amirka zata tafiyar da aikin gina gidaje da ba'a taba yin irinsa ba a duniya


Shugaba Bush na Amirka yayi alkawarin gudanar da wani gagarin aikin shirin gina gidajen zama mafi girma da wata gwamnati ta taba gudanarwa domin sake gine yankuna gabar Gulf da guguwar Katrina ta daidai ta. Yayinda yake jawabi ga al’umar kasa jiya Alhamis da dare, daga anguwa da ake kira French Quarters a birnin New Orleans, na jahar Louisiana, Mr Bush yace gwamnatin Tarayyar Amirka zata ginawa wadanda wannan bala’in ya afkawa gidajen zama, da samar musu ayyukanyi da wuraren kiwon lafiyarsu da kuma makarantu. Saida kuma shugaban bai bayyana adadin kudin da za’a kashe wajen gudanar da wannan aikin ba. To amma masu kididdigar ayyukan gine-gine da sake tsugunar da wadanda suka ta gayyara, sunyi hasashen cewa wannan aikin, kudin da zaici zai zarce dala Miliyon dari uku, kudin da tunin aka kashe kamansa a yakin Afghanistan da Iraq. Shugaba Bush yace yana fata ayanzu haka biranen Amirka sun kammala tanadin ka yadda zasu tinkari irin wannan bala’in, ko harin ta’addanci in sun zo musu. Shugaban yace ya umurci hukumar tsaron kasa akan ta nazarci irin shirye-shiryen da jihohi sukayi na tinkarar bala’inda ka sauko ba shiri a manyan biranensu. Mr. Bush ya kuma ce Amirkawa suna da damar ganin gwamnatin ta kyautata musu fiye da yadda akayi a wannan karon, don haka yace ya rungumi alhakin sakaci da akayi wajen kai dauki da wuri.

XS
SM
MD
LG