Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'yan Gwagwarmayar Nija Delta a Nigeria, sunyi barazanar  kona ma'aikatun haka da tatat Man Fetur a kasar.


Kungiyar 'yan gwagwarmayar Neja Delta ta Najeriya da ake kira Delta Volumteers Force ta yi barazanar cewa zata kokkona ma'aikatun Man Fetur na yankinsu idan gwamnati bata sako shugabansu daka kama aka tsare ba. Kungiyar ta baiwa Gwmnatin Najeriya wa'adin kwana daya tak data sako Muhahid Dokuba ko kuma ta yiwa ma'aikatan Mai kashedin cewa su fice daga yankin Neja Delta. Jiya Talata ce Kungyar tace 'yan sandan sun kama Mr Asari a birnin Potakwal suka kaishi birnin Abuja suka tsare. "yansansda kuma basu bada tabbaci akan sun kama shi ba. Ita kuma Kungiyar 'yan 'yakin sa kai na Ijaw Youth Council ta yiwa Ingila barazana a bayan da mahukuntan ingilan suka kama gwamnan jaharsu Diepreye Alamieyesiegha saboda zarginsa da satar hanyar shiga kasar da makudan kudi ba bisa ka'ida ba. Sunce sun kama wasu turawa biyu dake aiki wa kamfanonin mai aiki, kum sunce zasu kashe su in ba'a sako gwamnan su ba.

XS
SM
MD
LG