Yan yakin sa kai a Nigeria sun yi barazanar cunna wuta a ma’aikatun haka da tatar mai na Nigeria wani lokaci a yau Laraba idan har Gwamnatin kasar ba sako shugaban kungiyar da ta tsare ba. ‘Yan sandan Nigeria sunce suna rike da madugun ‘yan kungiyar Mujahid Dokubo Asari saboda yi masa tambayoyi bisa wasu kalamu da yayi na cin amanar kasar da neman tada zaune tsaye, a wata jaridar kasar mai fita rana-rana. “Yan sandan sunce sun dauki matakai na tabbatar da tsaron lafiya kuma suna tabbatarwa ‘yan Nigeria da baki cewa zasu kare wuraren samar da Ma’aikatun Man Fetur. Kungiyar Mr Asari ta ‘yan Kablar Ijaw da ake kira Niger Delta Volunteer Force, jiya Talata tayi barazana kuma tayiwa baki daki aikin Mai kashedin cewa suyi maza su fice daga yankin. “yan yakin sa kan sunce suna hobbasawa ne domin ganin sun sami kaso mai tsoka daga dukiyar da gwamnatin ke samu daga cinikin Man Fetur.