Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tace bazata janye daga alkawarin hana yaduwar....


Mataimakin shugaban kasar Iran Ghulamreza, Aghazadeh , yace kasarsa bata da niyar fita daga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, duk da gainin irin kokarin da kasashen yammaci keyi na ganin sun kai kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Mr. Agazade ya yi wannan kalamun ne a birnin Vienna bayan da ya kammala tattaunawa da wakilan kasashen Rasha da China da sauran kasashe dake halartan taron hukumar kula da sarrafa makamashi ta duniya I-A-E-A. Mataimakin shugaban Iran din wanda shine jagoran shirin sarrafa makamashi na Nukiliyar kasar Iran, yace ficewa daga wannan alkawarin baya cikin kudurorin kasarsa. Tun da fari babban mashawarcin kasar Iran din Ali Larijani yace tana wiywuwa kasar ta fice daga wannan yerjejeniyar, sannan da takaita binciken da jami’an hukumar makamashi zasu yi a kasar, muddin dai aka gabatar da ita a gaban kwamitin sulhu na MDD. Jakadu sunce Rasha da China da sauran kasashe sun nuna rashin amincewarsu ga kokarin gabatar da Iran gaban Majalisar Dinkin Duniya.

.

XS
SM
MD
LG