Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Rita ta sa mazauna Texas tashi alatilas su koma wani waje....


Dubun dubatan mazauna Jahar Texas da fargabar iskar Guguwar Rita ta tilastawa Kaura, sun sami kansu cikin wani cinkoson motoci da rashin Mai a kan mayan hanyoyin barin Jahar yayinda suke kokarin sake gari domin gudun bala'in wannan Guguwa ta Rita. Suna fama da tsananin zafin Rana akan hanyarsu. Hukumomi suna rarraba Mai ga wadanda Mai ya kare musu a mota. Labarin yace motoci sunyi jerin gwano na tsawon kilomita dari da sittin. Nan da sao'i 36 ne ake sarai Guguwar zata iso gabar jahar Texas. Gwamna Rick Perry na jahar yace wadanda suke kan hanya zasu tsere wa bala'i shigen irin wanda ya faru a jahar Louisiana makonni uku da suka wuce. Haka kuma filayen saukan jiragen sama suma suna fama da cunkoson fasinja dake niyar barin gari. Ma'aikatan kamfanonin sintirin jiragen sama suma sun arce tunin.

XS
SM
MD
LG