Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta cilla makamai masu Linzami kan Falasdinawa


Israila ta kaddamar da karin hare-hare da makamai masu linzami a zirin Gaza da safiyar yau litinin, jim kadan bayan da wani babban shugaban Hamas ya ce kungiyar ta daina kaima Israila hare-hare da rokoki. Babu labarin da aka tabbatar da sahihancin labarin game da wadanda su ka halaka ko jikkata sanadiyar hare-haren da Israila ta kai ta jiragen sama a Gaza da kuma Khan Younis. Rundunar sojojin Israila ta ce, ta kai hare-haren ne kan gine-ginen da kungiyoyin Palasdinawa ’yan gwagwarmaya ke yin amfani da su, su na kera makamai, ko kuma su na ajiye su. A jiya lahadi shugaban Hamas Mahmoud Zahar ya ce kungiyar ta tsaida hare-haren da ta ke kaiwa da rokoki, ya ce an dauki wannan mataki ne saboda a kare lafiyar al’ummar Palasdinawa. Ya bada wannan sanarwar ce wani lokaci bayan da wani harin da Israila ta kai da makamai masu linzami suka halaka Palasdinawa biyu, a ciki har da Mohammed Khalil wani jigo , kuma shugaban kungiyar Islamic Jihad. A wani al’amari na daban kuma, a yau litinin, rundunar sojojin Israila ta ce ta kama mutane 50, ’yan kungiyoyin Hamas da Islamic Jihad a yammacin kogin Jordan. Firayiministan Israila Ariel Sharon ya bada umarnin cewa, idan ya zama wajibi, sojojinsa su yi amfani da karfi akan ’yan gwagwarmayar kwatar ’yancin da aka dorama laifin harba rokoki masu dumbun yawa kan Israila, tun daga ranar Juma’ar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG