Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta kara kai hari kan Palasdinawa a yau Laraba


A yau Laraba sojojin Isra’ila sunci gaba da kai kazaman hare-hare kan ‘yan yakin sa-kan Palasdinawa a zirin Gaza. Sojin Isara’ilan sunce hare-haren da suke kaiwa ta jiragen sama suna auna gine-ginen da suka san ana shirya ayyukan ta’addanci a cikinsu ne. Wadannan hare haren sun janyo rashin wutan lantarki a zirin Gaza baki daya. Wani lokaci da safiyar yau ne Isra’ilan ta cilla makaman Atilari akan wasu wurare da ake harba mata rokoki daga arewacin zirin gazan. A yammacin kogin Jordan kuma, wasu shedu palasdinawa sunce sojin Is’rai’a sun kama wasu ‘yan kungiyar Jihadin Islama ta Hamas, yayinda hakan ta kara yawan wadanda ta kama zuwa dari hudu tun daga ranar Lahadi waccan. Shi dai wannan tashin hankalin ya zo ne bayanda wani abu mai kama da Bam ya fashe tsakanin kungiyar jihadin Islama ta Hamas a lokacin da suke taro a inda mutane 21 suka rasa rayukansu. “yan gwagwarmayar sun dora laifin fashewar kan Isra’ila, nan take suka dauki matakin ramuwar gayya, suka cilla Kokoki zuwa yankunan Kudancin Isra’ilan. To amma wani rahoto da masanan Palasdinawa da suka binciki gawarwarkin, suka bayar ya nuna cewa abinda ‘yan kungiyar hamas din suke gargin Isara’ila da shi, ba haka bane, binciken da sukayi ya nuna cewa burbudin da aka samu jikin mamatan, ya nuna cewa Kananan Rokoki, irin wanda ‘yan Hamas din ke curawa a gida shine ya fashe ya kashesu.

XS
SM
MD
LG