Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara kuri'ar raba gardama a Algeria


An fara kada kuri’ar raba garadama a Algeria kan shirin da gwamnatin ke yi na kawo karshen tashe tsahen hankula da ’yan kishin Islama suka haddasa na tsawon shekaru 13 da ya rutsa da sama da mutane dubu 120. Hukumomin kasar sunce sama da mutane miliyan 18 ’yan kasar Algeria ne suka cancanci kada kuri’a na goyon bayan shirin shugaba Abdel-Aziz Boute-flika ko mai adawa da shi. Shirin ya tanadi damar yin ahuwa ga 'yan tawayen da ke kurkuku ko wadanda ke gudun ceton rayukansu ko kuma wadanda ke kan fada har yanzu, amma banda wadanda suke da hannu dumu dumu wajen yiwa mutane da dama kisan gilla. Shirin ya kuma yi kira da a biya diya ga iyalan wadanda suka bace lokacin tashe tashen hankulan. Masu kushewa wannan dokar sunce wannan ba wani abu bane sai dabarar da shugaban kasar ke yi na yin kane kane bisa karagar mulki. Suka ce yin na’am da wannan dokar zai bada dama ga gwamnati ta gudanar da batun wadanda suka bace yayinda ake zargin cewa dakarun gwamnati na da hannu a bacewarsu. An shiga kai ruwa rana ne a Algeria shekara ta 1992 bayanda gwamnatin sojin dake mulki ta soke zaben yan majalisar dokoki da ake kyautata zaton yan kishin Islama ne zasu ci.

XS
SM
MD
LG