Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Kungiyar Kwallon Kafa Ta VOA Hausa Flamingos A Bauchi


Sashen Hausa na Muryar Amurka ya kaddamar da kungiyar kwallon kafa ta matasa mai suna "VOA Hausa Flamingos F.C." a garin Bauchi.

Wannan ita ce kungiyar farko daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na matasa da Sashen Hausa na Muryar Amurka zai ringa tallafawa, a wani yunkurin bayar da gudumawa ga habaka harkokin wasannin motsa jiki da rage zaman kashe wando a tsakanin matasa.

Ita dai kungiyar VOA Hausa Flamingos, wadda ake kira Bauchi Flamingos a da, shahararriyar kungiyar kwallon kafa ce ta matasa wadda sau hudu tana lashe kofunan wasannin matasa a Jihar Bauchi. Kungiyar ta taka rawar gani sosai a wasanni da dama kamar na Tarayyar Wasannin nMatasa ta Nijeriya, YSFON, da sauransu.

A yanzu haka kungiyar ta kai ga wasan kusa da karshe na cin kofin kwallon kafa na matasa na Nadada Umar a Jihar Bauchi, kofin da sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya bayar domin raya harkar wasannin matasa a cikin jihar.

XS
SM
MD
LG