Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Agaji Ya Fara Kaiwa Ga Dubban Mutanen Da Suka Tagayyara SAnadin Girgizar Kasa A Cikin Tsaunukan Himalaya a Pakistan


A yanzu dai agaji ya fara kaiwa ga dubban 'yan kasar Pakistan wadanda suka kubuta da rayukansu daga mummunar girgizar kasa, amma kuma su na fama da yunwa da tsananin sanyi. Jiragen helkwafta da motocin daukar kaya har ma da dabbobi kamar jakuna sun fara kaiwa cikin kauyukan dake cikin tsaunukan Himalaya wadanda kwanaki tara cur babu wanda ya samu kaiwa gare su.

A bayan da aka kwana biyu ana juye ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya hana jiragen saman agaji tashi, kyawun yanayi yau litinin ya sa jiragen sama masu saukar ungulu da yawa sun samu zarafin tashi suna karade tsaunukan na Himalaya inda ma'aikatan agaji suka yi gargadin cewa dubban mutane zasu mutu cikin ';yan kwanaki kadan idan ba su samu abinci, da tanti da barguna da kuma magunguna ba.

Jami'an kungiyar agaji ta Red Cross sun fadawa Muryar Amurka cewa har yanzu akwai wasu wurare kimanin talatin a yankin Kashmir bangaren Pakistan inda jiragen helkwafta ba zasu iya sauka ba, a saboda haka sai jeho kunshin kayayyakin agaji kawai suke iya yi daga sama. Suka ce mutanen wadannan yankuna suna kokarin giggina dandalin da jiragen na helkwafta zasu iya sauka a kai.

Amma kuma ana kara samun rahotannin mutuwa da barna a yayin gudanar da wannan gagarumin aikin agaji mai tattare da hatsari. Gwamnatin Pakistan ta ce yawan mutanen da suka mutu yanzu ya zarce dubu arba'in, amma kuma shugabannin yankin Kashmir sun ce adadin wadanda suka mutu ya zarce haka nesa ba kusa ba. Sun yi misali da wuraren da ba a ma fara tona gine-ginen da suka rushe ba, balle a gano gawarwakin dake karkashinsu.

XS
SM
MD
LG