Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Andakatar da zaman shawarwarin kawo zaman lafiyar  Sudan


Mashawarta dake tattaunawa domin kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin kasar Sudan dake gaba da juna sun dage zaman tattaunawarsu a dai-dai lokacin da aka sami karin tashe tashen hankula a yankin Dafur din. Tashin hankali na baya bayan nan sun dakatar da shirye shiryen kai kayakin agaji a yankin. Ana sa rai sai ranar 20 ga watan gobe na Nuwamba ne za’a sake komawa zauren taron wanda Kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta shirya shi tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kungiyoyin ’yan tawayen kasar. Taron farko da aka yi wata guda ana yinsa a Nigeria bai cimma wata nasarar kirki ba, musamman a bangaren rabon arzikin kasa da rabe raben mukamai. Yake-Yake da kuma a kai hare hare kan sojojin kiyaye zaman Lafiya na kasashen Afrika, sun dusasa zaman tattaunawar. A wannan makon MDD tace hare haren nan suna hana ayyukan agaji cigaba yayinda ala tilas suka tilatawa fararen hula yin hijira zuwa sansanonin da suke cike da mutane.

XS
SM
MD
LG