Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Shugaba Obasanjo Na Nijeriya, Stella, Ta Rasu a kasar Spain


Uwargida Stella Obasanjo, matar shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya, ta rasu yau lahadi a kasar Spain. Ta rasu tana da shekaru 59 da haihuwa.

Wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Remi Oyo, ta bayar, ta ce Uwargida Stella ta rasu bayan da aka yi mata tiyata a wani asibiti. Sanarwar ba ta bayar da karin haske ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Spain ta ce matar shugaban Nijeriya ta rasu yau lahadi da safe a wani asibitin dake garin shakatawa na Marbella a kudancin kasar inda ta kai ziyara ta kashin kai.

XS
SM
MD
LG