Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanar Theoneste Bagosora Ya Ce Neman Bata Masa Suna Kawai Ake Yi


Mutumin da ake zargin cewa shine ummul haba’isin kisan kare dangi da aka yi a kasar Rwanda a shekarar 1994 ya ce wannan zargi yunkuri ne kawai na neman bata masa suna.

A jiya litinin, Kanar Theoneste Bagosora, tsohon darektan ma’aikatar tsaro ta kasar Rwanda ya fara bayar da shaida a gaban Kotun bin Kadin laifuffukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya dake zama a kasar Tanzaniya.

Kanar Bagosora ya musanta kitsa kashe mutane dubu 800 ’yan kabilar Tutsi da masu tausaya musu daga cikin ’yan kabilar Hutu a madadin gwamnatin Rwanda. Masu gabatar da kararraki suka ce Kanar Bagosora ya umurci kwamandojin soja da su fara karkashe ’yan kabilar ta Tutsi jim kadan a bayan da shugaba Juvenal Habyarimana ya mutu a faduwar jirgin sama a watan Afrilun 1994.

Ana tuhumar Kanar Bagosora tare da wasu hafsoshin soja uku (Birgediya Janar Gratien Kibiligi, da Kanar Anatole Nsengiyumva da kuma Manjo Aloys Ntabakuze) da aikata kashe-kashen kare dangi da kuma cin zarafin bil Adama.

Kwamitin Sulhun MDD shine ya kafa kotun ta bin kadin laifuffukan yakin Rwanda a watan Nuwambar 1994. ya zuwa yanzu, kotun ta samu mutane 22 da laifi ta kuma sallami wasu mutanen su uku.

XS
SM
MD
LG