Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Sojojin Amurka Da Suka Mutu A Iraqi Ya Kai Dubu Biyu


Rundunar sojojin Amurka ta ce sojojin Amurka guda dubu biyu ne suka mutu a bakin daga a kasar Iraqi tun daga lokacin da aka kai wa kasar mamaya karkashin jagorancin Amurka a 2003.

Jami’ai suka ce mutuwa ta baya bayan nan ta wani soja ne da ya cika a sanadin raunukan da ya samu lokacin tashin bam a makon jiya a garin Samarra na yammacin kasar.

A halin da ake ciki, ’yan tawaye sun kashe mutane akalla 17 jiya talata a hare-haren da suka kai a Bagadaza da kuma birnin Sulaimaniyyah a arewacin kasar.

A cikin wata sanarwar da aka buga a wani dandali a duniyar gizo, sanarwar da babu hanyar tabbatar da sahihancinta, kungiyar al-Qa’ida ta Iraqi ta ce ta sace wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Morocco su biyu a Bagadaza. Jami’an Morocco sun bayar da rahoton bacewar mutanen biyu tun makon jiya.

Ita kuma hukumar zabe ta Iraqi ta bayar da sanarwar cewa fiye da kashi 80 daga cikin 100 na masu jefa kuri’a suka yi na’am da sabon daftarin tsarin mulki, matakin da ya share hanyar gudanar da babban zabe acikin watan Disamba. ‘Yan kallo na Majalisar Dinkin Duniya sun ce sakamakon kuri’ar raba-gardamar da aka yi a wannan watan na gaskiya ne babu magudi.

XS
SM
MD
LG