Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Ce Ba Su Yarda Shugaba Laurent Gbagbo Yaci Gaba Da Zama Kan Wannan Kujera Ba


’Yan tawayen Ivory Coast sun yi watsi da kudurin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da ya kyale shugaba Laurent Gbagbo ya ci gaba da zama kan kujerarsa na karin shekara guda.

’Yan tawayen sun fada cikin sanarwar da suka bayar jiya talata cewa zasu dauki shugaba Gbagbo tamkar mutumin da yayi juyin mulki idan har ya ci gaba da zama kan karagar mulki bayan cikar wa’adin shugabancinsa yau laraba 26 ga watan Oktoba.

Wannan sanarwa ta ’yan tawaye ta zo a daidai lokacin da jam’iyyun adawa na kasar ta Ivory Coast suka ce zasu janye daga cikin gwamnatin hadin kan kasa idan har Mr. Gbagbo bai sauka daga kan kujerar shugabancin kasar ba.

A halin da ake ciki, rundunar sojojin kasar ta ce zata fara rufe gadojin dake Abidjan birni mafi girma a kasar, yayin da ake fargabar barkewar zanga-anga ta ’yan adawa.

Da farko an shirya gudanar da zabe ranar 30 ga watan Oktoba, amma sai aka dage har sai illa ma sha Allahu a saboda matsalolin da aka fuskanta wajen shirya zaben.

Kwamitin Sulhun MDD da kuma Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka duk sun amince da kyale Mr. Gbagbo ya ci gaba da zama kan kujerar shugabancin kasar na karin shekara guda har sai an gudanar da sabon zabe.

XS
SM
MD
LG