Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Laurent Gbagbo Ya Lashi Takobin Ci Gaba Da Zama Kan Kujeraa Shugabancin Ivory Coast


Shugaba Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast ya lashi takobin ci gaba da zama kan wannan kujera, duk da arangamar da aka yi a tsakanin dakarun tsaronsa da 'yan adawa masu zanga-zangar nemansa da ya sauka daga kan wannan mukami.

Mr. Gbagbo ya fada jiya lahadi cewar zai ci gaba da zama kan kujerar shugabancin Ivory Coast a bayan cikar wa'adinsa na shekaru biyar da karfe 12 na daren lahadin da ya shige. Wani kuduri na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bai wa Mr. Gbagbo iznin kara yin watanni 12 a kan mulki domin shirya zabe.

Mr. Gbagbo ya ce zai yi bakin kokarinsa domin shirya zaben cikin shekara guda, ya kuma bayyana fatar cewa zai iya yin hakan tun ma kafin cikar shekara gudan.

A halin da ake ciki, 'yan tawayen kasar sun ayyana madugunsu, Guillaume Soro a zaman sabon Firayim minista. Shugaba Gbagbo ya ce zai nada firayim minista a cikin 'yan kwanaki kadan.

Tun da fari a jiya lahadi, sojojin sun yi harbi na kashedi, suka kuma harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa 'yan zanga-zangar ad suka doshi fadar shugaban kasa a birnin Abdijan domin neman Mr. Gbagbo da ya sauka.

XS
SM
MD
LG