Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Ta Ce Jami'an Tsaron Nijeriya Suna Yawaita Kashe Fararen Hula Wadanda Ba Su Dauke Da Wani Makami A Yankin Niger Delta


Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Amnesty International" ta ce a kokarinsu na kare cibiyoyin mai, dakarun tsaron Nijeriya suna yawaita kashe fararen hula wadanda ba su dauke da makamai.

Kungiyar Amnesty ta fada cikin wani rahoton da ta bayar yau alhamis cewa an kyale dakarun tsaro a yankin suna kashe mutane tare da lalata kauyuka da tsangayoyi ba tare da tunani ba.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta kafa wata hukuma mai zaman kanta domin ta binciki wannan cin zarafi. Har ila yau ta ce su ma kamfanonin mai na kasashen waje dake aiki a yankin suna da nasu alhakin na keta hakkin jama'a da ake yi, kuma ya kamata su dauki matakan inganta wannan lamari.

Rahoton yayi magana musamman a kan wani lamarin da ya faru inda jami'an tsaro suka kashe mutane 17 lokacin da suka kai farmaki kan wani kauye mai suna Odioma a watan Fabrairu. Ta ce dakarun tsaron suna farautar wasu 'yan daba ne dake dauke da makamai, amma kuma babu ko dayansu da aka kama a lokacin.

XS
SM
MD
LG