Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asibitocin Ethiopia Sun Ce An Kashe Mutane Kimanin 23, Wasu 150 Suka Ji Rauni Jiya Laraba


Asibitoci na Ethiopia sun ce an kashe mutane kimanin 23, wasu 150 suka ji rauni jiya laraba, a rana ta biyu a jere da aka shafe ana gwabzawa a tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar rashin yarda da sakamakon zaben watan Mayun da ya shige.

Dakarun tsaro sun yi harbi domin tarwatsa magoya bayan jam'iyyun hamayya dake jifa da duwatsu a birnin Addis Ababa.

'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da dama da kuma shugabannin adawa, cikinsu har da shugaban babbar jam'iyyar hamayya mai suna "Coalition for Democracy and Unity."

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi tur da wannan tashin hankali na 'yan sanda da kluma abinda ta bayyana a zaman yunkurin wasu 'yan adawa na tsokano tashin hankalin.

'Yan adawa sun ki yarda da sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki na watan Mayu, suna masu zargin cewa an tabka magudi.

Jiya laraba da maraice, daruruwan 'yan Ethiopia sun yi zanga-anga a tsallaken fadar White House a daidai lokacin da shugaba Bush yake karbar bakuncin Yarima Charles na Britaniya.

Masu zanga-zangar sun yi ta ikirarin cewa 'yan Ethiopia suna mutuwa a saboda kwadayin ganin dimokuradiyya, sun kuma bukaci shugaba Bush da ya buga waya ma firayim ministan Ethiopia, Meles Zenawi.

XS
SM
MD
LG