Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukaddashin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yana Afirka


Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka, Robert Zoellick, yana kasar Kenya, inda a yau talata zai fara tattaunawa da shugabannin babbar kungiyar ’yan tawayen yankin Darfur na yammacin Sudan. Wakiliyar Muryar Amurka, Meredith Buel, ta ce rangadi na baya-bayan nan na Mr. Zoellick zai mayar da hankali ne kan batun kasar Sudan, inda yake kokarin karfafa shirin tsagaita wuta mai neman wargajewa a yankin Darfur.

Har ila yau yana shirin lallashin gwamnatin Sudan da tsoffin ’yan tawayen kudancin kasar da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka rattabawa hannu a farkon wannan shekara. Yakin basasar shekaru 21 a kudancin kasar Sudan ya kashe, ko kuma ya haddasa sanadin mutuwar mutane kimanin miliyan biyu.

Amma kuma rikicin da ake yi yanzu a yankin Darfur shine yake neman shawo kan yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin gwamnati da ’yan kudancin kasar.

Ya zuwa yanzu, shawarwarin neman zaman lafiyar da aka gudanar har sau shida a Abuja, babban birnin Nijeriya, ba su kawo karshen fada ba.

Mr. Zoellick ya fadawa ’yan jaridar dake tare da shi kafin su sauka a kasar Kenya cewa akwai hatsari tattare da fadan da ya kaure cikin ’yan kwanakin nan a Darfur, yana mai fadin cewa, "Wannan sabon fada yana iya warware shirin tsagaita wutar da bai zauna daram ba a Darfur. A nan ma tilas ne mu shawo kan sassan su mutunta shirin tsagaita wuta, su kuma bullo da matsayi mai ma’ana da zasu tattauna kai a teburin shawara. Idan an koma ga yin shawarwari a ranar 20 ga watan Nuwamba, muna bukatar ’yan tawaye da gwamnatin hadin kan kasa su cimma tazara wajen kulla yarjejeniyar sulhu, a saboda fada da kashe kashe ba zasu warware rikicin ba."

Tun farkon 2003 kungiyoyin ’yan tawaye karkashin jagorancin kungiyar "Sudan Liberation Army" suke yakar sojojin sa kai da ake kira Janjaweed masu goyon bayan gwamnati a yankin Darfur.

Sojojin kiyaye zaman lafiya kusan dubu 7 na Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka sun shiga yankin, amma kuma mukaddashin sakataren harkokin wajen na Amurka ya ce wannan ba shi ne zai warware rikicin ba, yana mai cewa, "Abinda wadannan sojoji zasu iya yi kawai shine tabbatar da yin aiki da shirin tsagaita wutar da bai dore ba har zuwa lokacin da za a kulla yarjejeniyar sulhu. A saboda haka nake kokarin jaddada bukaar dake akwai ta ganin an yi an gama shawarwarin neman zaman lafiya. A saboda idan ba an kulla yarjejeniyar sulhu ba, mutane miliyan biyu zasu ci gaba da zama a sansanoni, ga ’yan janjaweed ba a karbe musu makamai ba, saboda haka babu wanda zai iya komawa gida."

Mr. Zoellick yana fatar ganin kungiyoyin tawaye na Darfur sun hada kawunansu, tare da lallashinsu da su yarda da matsayi guda idan an koma ga shawarwarin neman zaman lafiya da gwamnatin Sudan a nan gaba cikin wannan wata.

XS
SM
MD
LG