Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 57 A Kasar Jordan


'Yan harin kunar-bakin-wake sun kashe mutane akalla hamsin da bakwai a kasar Jordan, suka raunata wasu fiye da 100 lokacin da suka kai hare-hare kan wasu hotel-hotel uku a birnin Amman. Wadannan hare-hare sun abku kusan lokaci guda da misalin karfe 9 na daren laraba agogon birnin Amman.

An kai wadannan hare-hare a hotel din Hyatt da Radisson da kuma Days Inn. Masu magana da yawun ’yan sanda sun ce hare-haren bam din na kunar bakin wake ne. Majiyoyin tsaro sun ce hare-haren sun yi kama da irin na kungiyar al-Qa’ida.

Mukaddashin firayim ministan Jordan ya fadawa gidan telebijin na CNN cewar da alamun biyu daga cikin ’yan harin bam din suna sanye da rigunan kunar bakin wake da aka cika da bama-bamai, yayin da na ukunsu kuma ya tuka mota shake da bama-bamai.

Rahotanni daga birnin Amman sun ce akasarin barnar da aka gani a cikin hotel-hotel din ne ba wai a wajensu ko kofofinsu ba. ’Yan kasashen yammaci suna yawaita zuwa ko zama a wadannan hotel-hotel, amma hukumomin Jordan sun ce akasarin wadanda suka mutu Jordaniyawa ne.

Bam din da aka dasa a hotel din Radisson ya tashi a tsakiyar wani dakin taro a daidai lokacin da ake gudanar da wani bukin aure a ciki.

Sarki Abdullahi na Jordan ya ce wadannan ayyukan ta'addanci ne da aka kai kan fararen hular da ba su san fari ba, balle baki. Sarkin ya katse ziyarar da yake yi a kasar Kazakhstan ya doshi gida a bayan hare-haren.

A bayan fashe-fashen ’yan sanda da sojojin Jordan sun killace unguwannin dake kewaye da wadannan hotel-hotel. Hotel din Grand Hyatt da na Radisson suna wata unguwar da ake kira Jabal Amman, inda akwai manya-manyan hotel-hotel da kuma ofisoshin jakadancin kasashe da dama. Hotel din Days Inn yana unguwar Rabiyah a kusa da ofishin jakadancin Isra’ila.

Wani rahoton da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ce Jordan ta rufe bakin iyakokinta na kasa har sai illa ma sha Allahu.

Wannan shine hari mafi muni a kasar Jordan cikin ’yan shekarun nan. A cikin shekaru biyar da suka shige, hukumomin Jordan sun ce sun tono kungiyoyin ta’addanci da yawa da kuma makarkashiyar kai hare-hare na ta’addanci. A cikin watan Oktoba, wani harin roka da aka kai a tashar jiragen ruwan Aqaba dake bakin bahar Maliya yayi kusan samun wasu jiragen ruwan yaki guda biyu na Amurka dake tsaye a can. Daya daga cikin rokokin da aka harba ya fada kan wani dakin ajiye kayayyaki na soja dake kusa da nan ya kashe sojan kasar Jordan daya.

Jordan tana daya daga cikin manyan kawayen Amurka a gabas ta tsakiya. Ta zamo babbar hanyar da ma’aikatan kasashen waje ke bi domin shiga Iraqi. Iyalan Saddam Hussein da dama da jami’an gwamnatinsa sun koma kasar Jordan da zama tun bayan ad Amurka ta tumbuke gwamnatinsa a 2003. Wasu attajiran na Iraqi ma sun gudu sun koma can domin tserewa tashin hankalin da ake yi a kasarsu.

XS
SM
MD
LG