Wani sanannen dan jam'iyyar Republican a majalisar dattijan Amurka, ya ce martabar Amurka zata zube a idanun duniya idan har ta fara azabtar da mutanen da ta kama.
A lokacin da yake magana cikin wata hira da gidan telebijin na CBS, sanata John McCain, ya ce mutuncin Amurka ya zuba a duniya a bayan da aka fallasa irin cin zarafin da ake yi wa fursunoni a gidan kurkukun Abu Ghraib. Ya kara da cewa tilas Amurka ta tabbatar da cewa ba ta azabtar da mutane.
Sanata McCain shine marubucin kudurin dokar da zata haramtawa Amurka azabtar da fursunonin da ta kama, kudurin da majalisar dattijai ta amince da shi da gagarumin rinjaye a watan da ya shige.
Fadar White House ta yi barazanar hawa kan kujerar-na-ki a game da wannan kudurin doka, amma kuma mai bayar da shawara a kan harkokin tsaron kasa, Stephen Hadley, ya fada jiya lahadi cewar gwamnatin Bush tana aiki tare da sanatoci domin gyara kalmomin dokar ta yadda zata biya bukatun sanatocin tare da kare Amurka daga hare-haren ta'addanci.
Mako guda da ya shige a kasar Panama shugaba Bush ya yi ikirarin cewa Amurka ba ta azabtar da mutane.