Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidaya Kuri'u A Zaben Shugaban Kasa A Burkina Faso


An rufe tasoshin zabe an kuma fara kidaya kuri'u a kasar Burkina Faso, inda masu jefa kuri'a a wannan kasa dake Afirka ta Yamma suka zabi shugaban kasa.

Shugaban hukumar zaben kasar, Moussa Michel Tapsoba, ya ce an gudanar da wannan zabe sumul. Ana sa ran za a dauki kwanaki da dama kafin a samu cikakken sakamako.

Ana sa ran cewa shugaba Blaise Compaore, mai neman wa'adi na uku a kan karagar mulki, zai lashe wannan zaben cikin sauki. Wasu 'yan takara na jam'iyyun hamayya sun soki tsayawar da yayi a wannan zabe, suna masu fadin cewa yin haka ta karya tanadin tsarin mulki cewar wa'adi biyu kawai mutum zai yi a kan mulki. Amma kuma wata kotu ta kyale shugaban da ya yi takara.

Mr. Compaore ya hau kan karagar mulki a sanadin juyin mulkin da yayi shekaru 18 da suka shige. An zabe shi ba tare da hamayya ba a 1991, aka kuma sake zabensa da gagarumin rinjaye a 1998.

XS
SM
MD
LG