Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Blaise Compaore Ya Lashe Zabe A Burkina Faso


Jami'an zabe a Burkina Faso sun ce shugaba Blaise Compaore ya lashe wa'adi na uku a kan kujerar shugabancin kasar cikin sauki.

Cikakken sakamakon da hukumomi suka bayar ya nuna cewa Mr. Compaore ya lashe kashi tamanin daga cikin dari na kuri'un da aka jefa a zaben ranar lahadi da ta shige.

Mutumin da ya zo na biyu daga cikin 'yan takara 11 da suka kalubalanci shugaban, Benewende Sankara, ya samu kashi biyar daga cikin dari na kuri'un ne kawai.

A yayin da ake kidaya kuri'un, 'yan takarar jam'iyyun adawa sun yi zargin cewa an tabka magudi. Sun yi zargin cewa Mr. Compaore ya kafa wani tsari mai karfi na yin zamba a lokacin zaben.

Kungiyar yakin neman zabe na shugaban ta musanta wannan zargi.

'Yan kallo na kasa da kasa sun ce an gudanar da wannan zabe cikin lumana, cikin btsari, kuma a bisa dukkan alamu ba tare da ha'inci ba.

Har ila yau wasu 'yan takara na jam'iyyun adawa sun kushe yadda Mr. Compaore ya nemi wa'adi na uku a kan karagar mulki, suna masu fadin cewa wannan ya sabawa tanadin da tsarin mulki yayi na wa'adi biyu kawai. Amma kuma wata kotu ta bai wa shugaban iznin tsayawa takara a wannan zabe.

XS
SM
MD
LG