Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yana Shirin Ganawa Da Shugaba Hu Jintao da Firimiya Wen Jiabao Na Kasar Sin


Shugaba Bush yana kasar Sin, inda yake shirin ganawa da shugaba Hu Jintao da firimiya Wen Jiabao, a yayin da ya kai tsakiyar rangadin da yake yi a kasashen Asiya.

Mr. Bush ya fada cikin wani jawabin da aka yada ta gidajen rediyon Amurka asabar din nan cewa yana sa ran tattauna batun cinikayya da shugaba Hu. Ya ce taron kolin Kungiyar Hadin Kan tattalin Arzikin Kasashen Asiya da Pacific da ya halarta a ranakun alhamis da jumma'a ya nuna cewa kasashen Asiya sun zage damtse wajen ganin an wanzar da tsarin walwalar cinikayya a duniya.

Wani kakakin shugaban ya ce har ila yau Mr. Bush yana shirin tattauna shirin nukiliya na kasar Koriya ta Arewa da kuma kara sakarwa da al'ummar kasar Sin mara. Zai halarci wani taron ibada da za a gudanar a cikin wata majami'ar da gwamnatrin Sin ke gudanarwa. Daga bisani a gobe lahadin zai yi hawan keke tare da 'yan wasa na kasar Sin dake shirin halartar wasannin motsa jiki na Olympics.

A Koriya ta Kudu asabar din nan, Mr. Bush yayi jawabi ga sojojin Amurka a sansanin mayaka na Osan, inda ya ce sojojin na Amurka za su ci gaba da zama a Iraqi har sai sun samu nasara.

XS
SM
MD
LG