Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indonesiya Ta Ce Dan Kasar Na 12 Ya Kamu Da Murar Tsuntsaye


Indonesiya ta bayar da rahoton dan kasarta na 12 da aka samu da murar tsuntsaye, ta kuma ce nan da 'yan watanni kadan zata fara sarrafa maganin "Tamiflu" domin yakar wannan cuta.

Jami'an kiwon lafiya na Indonesiya sun tabbatar da cewa an samu wani yaro dan shekaru 16 da haihuwa da jinsin kwayar cutar ta murar tsuntsaye mai kisa "H5N1". Mutane bakwai da suka kamu da murar tsuntsaye a Indonesiya sun mutu.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce Indonesiya tana fatar fara sarrafa maganin "TAMIFLU" cikin watanni biyar domin biyan bukatun kasar ko da za a samu barkewar annobar wannan cuta.

Ita ma Taiwan ta ce zata fara sarrafa maganin "TAMIFLU" nata na kanta idan har wanda ta saya daga kamfanin sarrafa magunguna na kasar Switzerland, Roche (wanda ya kirkiro wannan magani), ya kare. Ofishin kare hakkin mallakin abinda mutum ya kirkiro ya fada ranar jumma'a cewar zai nemi lasisi ko iznin sarrafa wannan magani daga kamfanin na Switzerland.

Kamfanin Roche dai ya bayyana mamakin wannan sanarwa, yana mai fadin cewa kamfanin sarrafa magunguna na Taiwan ba zai iya sarrafa maganin cikin gaggawa kamar Roche ba, ba kuma zai iya sarrafa shi da rahusa ba.

XS
SM
MD
LG