Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Koma Ga Zirga-Zirga A Bakin Iyakar Gaza Wadda Ta Hada Falasdinawa Da Masar Da Sauran Duniya


Asabar din nan ne aka koma ga yin zirga-zirga a bakin iyakar Gaza wadda ta hada Falasdinawa da kasar Misra da kuma sauran duniya baki daya.

Jami'an Falasdinawa suka ce da karfe 12 na rana agogon yankin (karfe 11 na rana agogon Nijeriya) matafiyan farko zasu fara wucewa ta tashar bakin iyaka dake Rafah. Majalisar mulkin kan Falasdinawa ta yi bukin bude bakin iyakar a ranar Jumma'a.

Za a ring yin aiki da tashar bakin iyakar na tsawon sa'o'i hudu kawai a kowace rana, har sai dukkan 'yan kallo guda 70 na kasashen Tarayyar Turai sun isa can. A wani bangare na yarjejeniyar da Amurka ta shiga tsakani aka cimma, babu wani dan Isra'ila da zai zauna a bakin iyakar, amma kuma wata kungiyar hadin guiwa ta Isra'ila da Falasdinawa zata sa idanu a kan kai da komowa a bakin iyakar ta hanyar kyamarorin da za a kakkafa a tashar.

Isra'ila ta rufe bakin iyakar a watan Satumba a bayan da ta janye daga Gaza, kuma tun lokacin ta ki yarda ta bude bakin iyakar, tana mai bayyana fargabar cewa za a yi fasa kwabrin shiga da makamai zuwa cikin Gaza daga Misra.

XS
SM
MD
LG