Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya Ta Hana Bakin Haure Dubu Arba'in Tsallakawa Zuwa Turai A Wannan Shekarar


Wani babban jami'in Libya ya ce kasarsa ta hana bakin haure fiye da dubu arba'in tsallakawa zuwa Turai a wannan shekara kawai.

Ministan harkokin cikin gida, Naser al-Mabrouk, shi ya bayyana wannan a birnin Rum a lokacin wani taron 'yan jarida na hadin guiwa da takwaran aikinsa na kasar Italiya, Giuseppe Pisanu.

Mr. Mabrouk yayi rokon da a samu hadin kan kasashen duniya wajen takalar matsalar bakin haure, ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata kasarsa ta dauki nauyin gudanar da taron kasashen duniya a kan wannan batu.

Bakin haure daga Afirka da Gabas ta Tsakiya sun mayar da Libya ta zamo zango mafi a'ala a yunkurinsu na tsallaka tekun bahar Rum zuwa cikin Turai domin neman ayyukan yi.

XS
SM
MD
LG