Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Zimbabwe Suna Zaben 'Yan Majalisar Dattijai Asabar Din Nan


Asabar din nan ne 'yan Zimbabwe suke zaben wakilan sabuwar majalisar dattijai, amma masu fashin bakin siyasa sun ce suna tsammanin akasarin masu jefa kuri'a miliyan uku da dubu dari biyu na kasar zasu kauracewa rumfunan zabe.

Masu fashin baki sun ce ko ohon masu jefa kuri'a da tsadar gudanar da bangaren majalisar dokoki da kuma fadar cikin gida a babbar jam'iyyar adawa ta "Movement for Democratic Change" sune zasu kashe guiwar masu jefa kuri'a su kauracewa zaben.

An samu baraka a cikin jam'iyyar MDC a bayan da ta jefa kuri'ar shiga cikin zaben. Shugaban jam'iyyar, morgan Tsvangirai, ya sa kafa ya shure wannan shawara, ya kuma kori 'ya'yan jam'iyyar su 26 wadanda suka ki jin kiran da yayi musu na su janye daga yin takara a zaben.

daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar ta MDC, Tendai Biti, ya ce ya kamata jam'iyyar ta kauracewa zaben, yana mai fadin cewa ba za a yi wannan zabe cikin adalci ba. Wadanda ke goyon bayan shiga zabe a cikin jam'iyyar sun bayyana fargabar cewa ta hanyar kauracewa zaben, za a kara mayar da jam'iyyar saniyar ware a harkokin siyasar kasar.

An kirkiro da sabuwar majalisar dattijan ne a bayan gyaran da aka yi ga tsarin mulkin Zimbabwe a cikin watan Maris.

XS
SM
MD
LG