Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar PDP a Najeriya ta kori  gwamna jahar Bayelsa


Jam'iyar PDP dake rike da ragamar mulkin Nigeria ta kori gwamnan jihar Bayelsa wanda yayi shigar mata a watan jiya ya tsere daga kasar Ingila bayanda aka bada belinsa ya koma gida Najeriya. A jiya Alhamis ne jam'iyar PDP ta bayyana cewa abinda gwamna Diepreye Alamieseigha yayi abinda ya janyowa jam'iyar PDP cin zarafi da kunyatarwa ainun. A makonin baya ne aka cafke wannan gwamna a can Ingila aka tuhumeshi da laifin tara kudaden haram da suka zarce dala miliyon 3 a gidansa da kuma ajjiyasa a banki, wadanda akace kudadden sata ne na gwamnatin Nigeria. A makon jiya ne yayi shigen mata inda ya saka rigar mata harda hular gashi na jebu irin na mata kana yayi amfani da fasfo na karya dake dauke da sunan wata mace ya saci hanya ya fita daga kasar Ingila.

XS
SM
MD
LG