Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saddan Husaini yaki shiga Kotu a yau Laraba


Karin wasu shedu biyu sun dada bada sheda a gaban kotun dake shara’ar tsohon shugaban Iraq Saddam Hussein tareda wasu mukarabansa su bakwai, wadanda kuma dukkansu ake zarginsu da kashe mutane ‘yan shi’a su fiyeda 140 kamar shekaru 23 da suka wuce. Shari’ar, wacce ake nuna ta ta yayinda ake yinta, an makara wajen fara ta a yau bayanda Saddam Husseini yaki zuwa kotun saboda wulakancin da yace ana nuna mishi. Daya daga cikin shedu da ya bayyana amma wanda aka ki bada sunansa, yace an taba tsare shi kwana da kwannaki ba tareda an bashi abinci ko abin sha ba na tsawon kwannakin da yayi a tsare. Shi dai Saddam Husseini da mukarabban nashi duk ana zarginsu ne da laifin bada umurni a kashe mutane a garin Dujali na can Iraq da farmaki bayan yunkurin da aka yi na kashe shi a 1982. Yanzu dai alkalin kotun, Rizgar Mohammed Amin ya dage zaman kotun na tsawon makkoni biyu, har zuwa ran 21 ga watan nan, ta yadda za’a baiwa jama’a damar shiga zaben ‘yan majalisan dokokin da za’ayi a ran Alhamishin makon gobe.

XS
SM
MD
LG