Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan kasar Kongo Kinshasa da dama sun arecewa yaki


Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sunce dubban dubatan mutanen kasar Junhuriyar demokradiyar Congo-Kinshasha na can suna ta arcewa, suna barin gidajensu, saboda kazancewar yakin da ake gwabzawa tsakanin sojan gwamnati da dakarun kungiyoyin ‘yantawaye. Yanzu haka ma jami’an ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da raba kayan agaji yace kamar mutane dubu 25 suka rasa muhallinsu a sanmadin wannan yakin da tun cikin watan jiya na Nuwamba ake yinsa a cikin lardin Katanga. Suka ce daga lokacin zuwa yanzu, mutanen da suka rasa muhallinsu sun kusa kai dubu 100. A kwanan nan ne dai rundunar sojan ta Congo ta daura damarar ganin bayan wata rundunar ‘yan banga da ake kira “Mai Mai’. Ita gwamnatin ta Congo tana son kasar baki dayanta ta koma hannunta ta yadda komai zai tafi daidai a kasar kafin zaben da za’ayi kwanan nan a kasar, wanda shine zabe na farko a cikin fiyeda shekaru 40 da suka wuce. Allah kadai Ya san ko mutane milyan nawa aka hallaka yakin basasar da aka share shekaru biyar ana yi a Congo, wanda sai a shekarar 2003 aka gama shi.

XS
SM
MD
LG