Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chadi Ta Ce Dakarunta Sun Fatattaki Harin 'Yan Tawaye A Wani Gari A Kusa Da Bakin Iyaka Da Sudan


Gwamnatin Chadi ta ce sojoji sun fatattaki wani harin da 'yan tawaye suka kai a wani gari dake bakin iyakar kasar ad Sudan.

Ministan sadarwa na Chadi, Hourmadjo Moussa Doumgor, ya ce an kashe mutane kimanin 100 a wannan fada da aka gwabza a kusa da garin Adre dake bakin iyaka a gabashin kasar, mai barikin soja, sai dai babu wata kafar da ta tabbatar da hakan.

Ma’aikatan agaji a yankin sun ce suna jinyar mutane kimanin dozin guda da suka ji rauni.

Jami’an Chadi sun ce suna da ikon bin sawun wadanda suka kai harin zuwa cikin kasar Sudan a yankin da ’yan tawayen Darfur suke yakar gwamnatin Sudan. An yi imanin cewa ’yan tawayen da suka kai harin sun hada har da wasu sojojin da suka gudu daga cikin rundunar sojojin Chadi, wadanda suka yi kiran da a hambarar da shugaba Idris Deby. An zarge su da laifin kai hare-hare cikin ’yan kwanakin nan a kan barikokin soja a Chadi, ciki har da na N’djamena babban birnin kasar, kafin su arce su koma gabas. An yi imani da cewa ’yan tawayen suna tattaruwa a bangaren Sudan na bakin iyaka.

Wani mai fashin baki na cibiyar nan mai suna "Global Insight" dake da cibiya a London, Chris Melville, ya ce wannan lokaci ne mawuyaci ga shugaba Deby, wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki shekaru 15 da suka shige. Mr. Melville ya ce, "barazanar da gwamnatinsa take fuskanta tana ninkuwa cikin gaggawa. Gujewar da wasu sojoji suka yi a baya bayan nan daga cikin rundunar sojojin kasar ta nuna cewa irin adawar da shugaba Deby yake fuskanta daga cikin gwamnatinsa tana kaiwa wani matsayi mummuna.

Mr. Melville ya ce wannan karuwar rashin kwanciyar hankali na zuwa a daidai lokacin da gwamnatin Idris Deby take kara fuskantar wahala wajen kula da dubun dubatan ’yan gudun hijira da suka tsere daga yankin Darfur na kasar Sudan, yana mai cewa, "Ba wai matsalar ’yan gudun hijira a yankin gabashin Chadi ce ta haddasa matsalolin da shugaba Deby yake fuskanta a yanzu ba, amma kuma a zahiri ta taimaka wajen janyo masa matsalar kudi da kuma yadda ya kasa samun kudin kai farmaki na murkushe masu yi masa tawayen.

Gwamnatin Sudan ta yi kukar cewa wasu daga cikin ’yan gudun hijiran dake Chadi suna kafa wata sabuwar rundunar ’yan tawaye, suna kai farmaki kan cibiyoyin gwamnati a bakin iyaka. Mr. Deby yayi kokarin shiga tsakani domin sasanta rikicin Darfur tare da maido da tsaro a yankin, amma kuma kokarin da yake yi tare da na KTKA ba su kawo ga dakatar da fadan da ake gwabzawa ba.

XS
SM
MD
LG