Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamun Al'ummar Kwango-Ta-Kinshasa Sun Amince Da Sabon Daftarin Tsarin Mulki


Sakamakon zabe na baya-bayan nan daga Kwango-ta-Kinshasa ya nuna cewa masu jefa kuri'a sun yi na'am da sabon daftarin tsarin mulki da gagarumin rinjaye.

A bayan da aka kidaya fiye da kashi biyu cikin uku na kuri'un, jami'an zabe sun ce kashi 83 daga cikin 100 na masu jefa kuri'a sun yi na'am da kundin.

Tsarin mulkin zai share fagen gudanar da zabubbuka na kasa baki daya a shekarar 2006 tare da taimakawa wajen kawo karshen shekara da shekarun da aka yi ana fama da yake-yake da rashin kwanciyar hankali a kasar.

A halin da ake ciki, ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Kwango-ta-Kinshasa ya ce an kwace wani sansani na sojojin sa kai dake yankin gabashin kasar a ranar asabar, a wani farmakin hadin guiwa a tsakanin sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar da sojojin gwamnatin Kwango. Ofishin ya ce sojoji fiye da dubu daya da 800 ne suka shiga cikin wannan farmakin na kwato tungar 'yan tawaye a Nioka a lardin Ituri.

Duk da cewa an kawo karshen yakin basasar shekaru biyar a cikin shekarar 2003, har yanzu sojojin sa kai sun ci gaba da cin karensu babu babbaka a sassa da dama na kasar.

XS
SM
MD
LG