Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Rahoto Yace Satar Jin Wayoyi Da Karanta Wasikun Mutane Da Gwamnatin Bush Take Yi A Cikin Gida Ya Zarce Yadda Ta Fada


Har yanzu fadar shugaban Amurka ta White House ba ta ce uffan ba game da wani rahoton da aka buga cewar Hukumar Tsaro ta Kasa ta saci ganin wasikun da aka aika ta duniyar gizo, watau Email, tare da satar jin wayoyin tarho na jama’a a asirce duk ba tare da iznin kotu ba, fiye da yadda ita gwamnatin ta fito ta amince cewar ta yi.

Jaridar New York Times ta ambaci jami’an gwamnatin Amurka na yanzu da kuma tsoffi suna fadin cewa hukumar tsaron ta sa idanu da kunne a kan sakonni na cikin gida da na waje tare da taimakon kamfanonin sadarwa. Ba a bayyana sunayen kamfanonin da suka taimaka din ba, amma kuma an ce tun bayan hare-haren 11 ga watan satumbar 2001, sun yi ta tattara bayanai game da irin kiraye-kirayen waya na mutane.

Jami’an hukumar tsaron su kan duba bayanan mutanen da aka kira da irin abubuwan da aka fadi bisa fatar zakulo ’yan ta’adda.

Gwamnatin shugaba Bush tana fuskantar karin suka a saboda yadda take gudanar da ayyukan leken asiri ba tare da iznin kotu ba a cikin Amurka a kan abinda ta ce wayoyin tarho ne ko sakonnin Email daga Amurka zuwa kasashen waje ko daga waje zuwa nan Amurka.

Wannan aikin leken asiri a cikin gida ya tado da kayar baya daga ’yan majalisar dokokin tarayya.

XS
SM
MD
LG