A bayan da suka shafe shekaru kusan 7 suna gidan wakafi a kasar Libya, ma’aikatan lafiya ’yan kasashen waje su shida sun yi nasarar daukaka karar da suka shigar, inda aka soke hukumcin kisan da aka yanke musu.
Yanzu wata karamar kotu zata sake yi musu shari’a baki daya.
A shekarar 1999 aka kama ma’aikatan jinyar, watau nas-nas biyar ’yan kasar Bulgariya da wani likita Bafalasdine, tare da wasu mutanen, aka tuhume su da laifin sanyawa yara 426 ’yan Libya kwayar cutar nan ta HIV mai haddasa kanjamau ko SIDA.
An ce hamsin daga cikin wadannan yara sun mutu. Iyaye da wakilan wadannan yara sun nuna rashin yardarsu da hukumcin da kotun kolin ta yanke.
A lokacin shari’ar farko da aka yi musu a shekarar 2004, an samu wadannan ma’aikatan lafiya su shida da laifi aka kuma yanke musu hukumcin kisa ta hanyar harbewa.
Kwararru a fannin kiwon lafiya suka ce yaran sun fara harbuwa da kwayar cutar ta HIV tun kafin wadannan ma’aikata su isa wannan asibiti, kuma watakila rashin tsabta ce ta sa suka harbu. Ma’aikatan lafiyar suka ce an yi ta gana musu azaba har sai da suka yarda suka furta da bakunansu cewar sune suka sanyawa yaran kwayoyin cutar da gangan.
Alkalin da ya bi kadin daukaka karar jiya lahadi ya ce babu shakka akwai matsala kan yadda hukumomin Libya suka tafiyar da wannan shari’a.
Da farko Bulgariya ta ki yarda ta samar da agaji ga wadannan yara da suka harbu da cutar, amma kuma a ranar alhamis jami’ai sun bayar da sanarwar cewa zasu taimaka wajen kafa wani asusun da zai taimakawa yaran tare da taimakon Tarayyar Turai da Amurka.
Bulgariya ta yi marhabin da hukumcin a zaman alama mai karfafa guiwa, ta kuma bayyana fatar za a bi kadin wannan batu cikin gaggawa.