Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubbai Sun Ziyarci Bethlehem Domin Kirsimeti


Masu ziyarar addini su fiye da dubu 30 suka jurewa ruwan sama da sanyi mai tsanani da ake zubawa suka ziyarci kogon dake cikin Majami’ar Nativity inda aka ce an haifi Yesu,a birnin Bethlehem dake yankin Yammacin Kogin Jordan.Wannan adadi ya ninka yawan wadanda suka ziyarci birnin bara.

Fargabar tashin hankali ta sa maziyarta sun kauracewa birnin tun lokacin da Falasdinawa suka fara tayar da kayar baya a shekarar 2000, amma tsagaita wuta da kuma lafawar tashin hankali sun sa masu ziyarar addini sun kwarara zuwa birnin na Bethlehem a wannan Kirsimeti.

Daya daga cikin wadannan maziyarta shine Steven Augdinm daga Jihar Tennessee a nan Amurka. Mr. Augdin ya ce, "babu shakka kullum zaka ji wani labari na wannan yankin duniya, har ma sai mutum ya fara dari-darin zuwa. Amma kuma tun lokacin da muka zo da alamun zaman lafiya kuma babu fargaba."

Jamie Jon Pearson, wanda ke zaune a Jihar Utah, shi ma a nan Amurka, ya ce babu wani abinda ke tayar masa da hankali, domin kuwa a cewarsa, "wata baiwa ce mutum ya ziyarci wannan wuri. Sau daya mutum yake rayuwa a wannan duniya kuma na so in ziyarci wannan wuri akalla au daya domin Kirsimeti. A saboda haka farin ciki na da kuma wannan baiwa ta ziyartar wannan wuri sun sha kan duk wata fargaba ko tsoron da nake da shi."

Maziyartan sun tallafawa tattalin arzikin Bethlehem wanda ya dogara a kan masu ziyara. Nadia Hazboun tana lura da wani kantin sayar da kayayyakin gargajiya a dandalin Manger. Ta ce, "...bukin Kirsimeti na wannan shekara ya fi na shekarun baya. Ina jin cewa wannan shine Kirsimeti mafi amfani da muka gani a cikin shekaru biyar."

Sai dai kuma Falasdinawa suna murna tare da yin bakin ciki a wani gefen. A yayin da suke murnar ganin masu ziyarar addinin, sun yi amfani da wnnan dama ta ganin baki daga kasashen waje domin bayyana bacin ransu da katangar tsaron da Isra’ila take ginawa a wajen garin.

Magajin garin birnin Bethlehem, Victor Batarseh, ya fadawa Muryar Amurka cewar, "Ina bakin ciki. Abin kunya ne ga al’ummar duniya baki daya su kyale a gina wannan katanga wadda zata kewaye birnin da aka haifi Yesu, birnin Bethlehem. Yanzu birnin na Bethlehem ya zamo wani babban gidan kurkuku."

Isra’ila ta ce katangar tana hana ’yan harin kunar bakin wake shiga cikin kasrta. Amma kuma a cikin sakonsa na Kirsimeti, babban fada na mabiya darikar Katolika a Bethlehem wanda kuma Bafalasdine ne, ya ce abinda kasa mai tsarki take bukata a yanzu ita ce gadar da zata hade mutane, ba katangar ad zata raba tsakaninsu ba.

XS
SM
MD
LG