Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Yi Wa Ariel Sharon Tiyata


Za a yi wa firayim minista Ariel Sharon na Isra’ila tiyata a zuciya a wata mai zuwa.

Wakilin Muryar Amurka, Robert Berger, ya ce a cikin makonni biyu ko uku dake tafe, za a gudanar da aikin toshe wani dan rami da aka gano a zuciyar Mr. Sharon. Likitoci sun ce sun saba gudanar da irin wannan aiki, kuma ba wani abun damuwa ne ko kuma mai barazana ga rai ba.

Dr. Natan Borenstein ya ce wannan tiyata ba zata durkusar da firayim ministan ba, yana mai cewa, "Ina jin cewa Mr. Sharon zai koma bakin aikinsa, kuma ina jin cewa (aikin da za a yi masa) ba zai sa ya sauya yadda yake gudanar da rayuwarsa ba."

Amma kuma a yanzu shekarun Mr. Sharon 77 ne, kuma yana da kiba fiye da kima. An fara nuna karin damuwa game da lafiyarsa tun makon jiya a lokacin da ya hadu da toshewar babbar hanyar jini maras tsanani. Likitoci suka ce babu wata illa ta dindindin da ta same shi, amma kuma sun neme shi da ya rage kiba.

Ana kara damuwa da koshin lafiyarsa ne musamman ganin cewa yana fuskantar yakin neman zabe mai tsanani kafin babban zaben da za a yi a watan Maris.

Mai fashin bakin harkokin Isra’ila, Amotz Asa-El ya ce Mr. Sharon ba ya da magaji. Firayim ministan yana da farin jini da karfin hali, kuma shi ya janye Isra’ila daga Gaza, kuma ya ce a shirye yake ya janye daga wasu sassan na yankin yammacin kogin Jordan.

Abinda ’yan Isra’ila da dama suke fargaba shine babu wani wanda zai iya maye gurbinsa.

XS
SM
MD
LG