Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nuna Bacin Rai Da Tarzoma Game Da Sabuwar Gwamnatin Kasar Ivory Coast


Firayim ministan da aka nada kwanakin baya a kasar Ivory Coast, Charles Konan Banny, ya nada sabuwar gwamnatin da ya ce zata jagoranci kasar zuwa ga zabe a shekara mai zuwa. Sai dai kuma yayin da wasu ke yabawa, wasu suna kushewa sabuwar gwamnatin.

Magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo sun fantsama kan titunan birnin Abidjan a fusace ranar laraba a bayan da gidan rediyon gwamnati ya watsa sunayen sabbin nministoci.

Daruruwan matasa 'yan ta-kife dake kiran kansu "Young Patriots" sun girka shingaye suka kona tayu a bangaren birnin da ake dauka a zaman tungar magoya bayan shugaba Gbagbo. Dakarun tsaro sun tarwatsa taron, su na yin harbi a sama. Babban nkwamandan sojojin kasar, Janar Philippe Mangou, yayi rokon da a kwantar da hankula.

Wata mai goyon bayan shugaban, Patricia Hamza, ta ce matasan suna zanga-zangar nuna rashin jin dadin sanya wasu shugabannin 'yan tawaye biyu ne a cikin sabuwar gwamnati. Mrs. Hamza ta ce, "ba zamu yarda da wadannan mutane a cikin gwamnati ba...a saboda sune suka dauki makamai suka jefa mu cikin halin da muke a yanzu...."

Shi kansa firayim minista Charles Konan Banny zai rike mukamin ministan kudi. A da wannan mukami yana hannun wani mai goyon bayan shugaba Gbagbo ne.

Wani dan tsohuwar jam'iyyar dake mulkin kasar, Claude Ahobaut, yana da kwarin guiwa, kamar wasu shugabannin siyasa da dama, cewar gwamnatin Mr. Banny zata taka rawar gani.

Ya zargi 'yan bangar shugaba Gbagbo da ake kira "Young Patriots" da kokarin neman hana aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya da aka tsara da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru uku a kasar. Ya ce a yanzu tilas ne sabuwar gwmnati ta yi aiki da taswirar cimma zaman lafiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta zana sau da kafa. Shirin ya nemi da a kwance damarar yaki a kuma gudanar da zaben shugaban kasa a 2006.

Madugun 'yan tawayen arewacin kasar, Guillaume Soro, da mataimakinsa, Louis Dakoury Tabley, su na da kujeru a sabuwar majalisar ministoci.

Amma kuma wani kakakin 'yan tawaye, Cisse Sindou, ya ce magoya bayan Mr. Gbagbo su na da kujeru fiye da kima a sabuwar majalisar ministocin. Ya kuma ce tilas ne a kyale firayim ministan ya gudanar da aikinsa.

Yakin basasa ya barke a karshen shekarar 2002 a kasar Ivory Coast. Wata yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tare da taimakon Faransa a 2003 ta kirkiro da wani yankin da ya raba tsakanin sojojin 'yan tawaye a arewacin kasar, da sojojin gwamnati a kudu.

XS
SM
MD
LG