Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Yakubu Gowon Ya Ja Kunnen Obasanjo Game Da Yin Tazarce


Wani tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijeriya ya shawarci shugaba Olusegun Obasanjo da ya guji neman yin tazarce, ta hanyar neman wa’adi na uku a kan kujerar mulki, matakin da tsarin mulkin Nijeriya bai yarda ba.

Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya ce tilas shugabanni su gujewa kwadayin ci gaba da yin mulki domin yin hakan zai sa jama’a su tunzura da su.

Mr. Gowon ya kwace mulki a 1966 amma sojoji sun yi masa juyin mulki a 1975 bayan da ya bayyana shirin ci gaba da yin mulki fiye da ka’idar da ya tsayar tun da farko.

Jita-jita ta baza gari cewar Obasanjo yana da niyyar yin rub da ciki kan karagar mulkin Nijeriya a bayan wa’adinsa ya cika a watan Mayun 2007.

Cif Obasanjo ya ki ya fito da bakinsa ya musanta wannan rade-radi ko kuma ya gaskata. Amma kuma kalamun baya bayan nan daga bakin wasu shugabannin jam’iyyar PDP da kudurin da wani kwamitin majalisar dattijai ya gabatar sun nuna alamun cewar akwai wata kumbiya-kumbiyar da ake shirin yi ta kawar da tanadin wa’adi biyu kan kujerar mulki daga tsarin mulki, abinda zai share wa Obasanjo fagen sake yin takara.

XS
SM
MD
LG